Jami’in hukumar zabe mai zaman kanta na jihar Katsina (INEC) Ibrahim Zarewa ya bayyana cewa masu sa ido a zabe 2000 ne za su sa ido a zaben gwamna da na majalisar dokoki da za a yi a jihar ranar 9 ga watan Maris.
Zarewa ya sanar da haka ne ranar Alhamis da yake ganawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a garin Katsina inda ya kara da cewa daga masu sa ido a zabe 2000 din dake jihar kungiyoyi 51 daga kasashen waje da suka hada da Tarayyar Kasashen Afrika African (AU), Tarayyar kasashen Turai (EU), ECOWAS, ofishin jakadancin kasar Amurka da Britaniya.
Ya kuma ce hukumar zabe ta kammala raba duk kayan aikin zabe a Kananan hukumomi 34 inda daga nan ne za a rarraba wa mazabu 361 dake jihar.
Zarewa ya tabbatar da cewa hukumar ta dauki matakan da za su taimaka wajen ganin zaben ya gudana yadda ya kamata kuma akan lokaci.
‘‘Mun saita duk na’urorin tantance katin zabe domin gujewa matsalolin rashin aikin na’uran a ranar zabe sannan mun kammala hora da duk ma’aikatan da za suyi aiki a ranar.
A karshe Zarewa ya ce dan takarar jam’iyyar APC Aminu Masari, dan takarar jam’iyyar PDP Yakubu Lado Danmarke da wasu ‘yan takara 18 ne za su gwabza za zaben kujeran gwamna sannan ‘yan takara 316 ne za su yi kokuwan kujerun majalisar dokoki na jihar.