Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta fara raba kayan zabe a dukkan Kananan Hukumomi 44 na Jihar Kano.
Mataimakin Daraktan Hulda da Jama’a na INEC, Garba Lawal ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, yau Alhamis a Kano.
A cewar sa, ma’aikatan INEC sun fara tantance kayan zabe, musamman takardun kuri’a na kowace karamar hukuma tun ranar Laraba.
Lawal ya ce za a kammala raba dukkan kayan zaben a ranar Juma’a.
Ya ce daga nan zuwa Juma’a za a kammala raba kayyyakin yadda aikin zai yi wa jami’an INEC na wucin-gadi sauki kuma yadda za su iya isa wuraren aikin su da sassafe a ranar da za a gudanar da zabe, ranar Asabar.
JIHAR KADUNA
A jihar Kaduna ma Hukumar Zabe ta Kasa, INEC ta bada sanarwar ta kai kayan zabe a dukkan kananan hukumomi 23 da ke jihar domin zaben gwamna da na majalisar dokokin jihar.
Jami’in Hulda da Jama’a na INEC na jihar Kaduna, Sani Abdulfatah ne ya bayyana haka ga wakilin NAN na jihar Kaduna.
Ya ce an rigaya an ware kuma an tantance dukkan kayan aikin zaben na kananan hukumomin jihar 23, wadanda za a yi zabe da su mazabu 255 da kuma rumfunan zabe 5,102 da ke fadin jihar.