Zababben Sanatan Anabra ta Kudu, Ifeanyi Uba, ya karyata rade-radin da ake yi cewa ya fice daga sabuwar jam’iyyar da a karkashin ta aka abe shi, wato YPP, ya koma APC.
Uba, wanda shi ne mai kamfanin Capital Oil, ya ce har yanzu ya na nan daram a cikin jam’iyyar da aka zabe shi, wato YPP.
Jaridu da dama a ranar Litinin sun ruwaito cewa Uba ya tuma tsalle ya koma APC, tun ma kafin a kai ga rantsar da shi a matsayin sanata.
Amma da ya ke magana da PREMIUM TIMES, kai-tsaye ta wayar tarho a jiya Talata, Uba ya ce ya na da kusanci da APC, amma fa bai koma cikin jam’iyyar ba.
“A kan me zan koma APC? Babu wata rigima da ke faruwa a cikin YPP. Abinda kawai ya faru shi ne, shugaban jam’iyyar APC ne a wurin wata liyafar cin abinci, ya gabatar da ni a matsayin wanda ke kan hanyar komawa APC, inji shi. To ka ga ai bai kamata ya yi wannan maganar ba, a matsayin sa na shugaban jam’iyya.”
Uba ya kara da cewa a zaman yanzu ana kalubalantar nasarar sa kotu, amma fa har yanzu ya na cikin YPP bai fita ba.
“Su Sanata Andy Uba, kanin sa Chris Uma da Umeh su na kalubalantar nasara ta a kotu. To ina rara-gefe a cikin APC, amma fa ban koma ba, ban fice daga YPP ba.”
“Sai dai abin da na ke so na fahimtar da jama’a shi ne, bai yiwuwa na kasance ni kadai ne dan jam’iyyar YPP a cikin Majalisar Dattawa.
Ko dai na goyi da bayan babbar jam’iyyar Adawa, PDP ko kuma na goyi da bayan bangaren jam’iyya mai mulki, APC. Amma hakan ba ya na nufin na koma a cikin kowace jam’iyya ce na jingina da ita ba.”