Za a kirkiro karin hanyoyin karbar haraji ga ’yan Najeriya –Ministar Kudi

0

Gwamnatin Tarayya ta kammala dukkan shirye-shiryen da suka kamata, domin bijiro wa ‘yan Najeriya da sabbin hanyoyin karbar haraji.

Ministar Harkokin Kudade Zainab Ahmed ce ta bayyana haka, inda ta ce za a bijiro da hanyoyin ne domin samar wa gwamnati kudaden shiga.

Zainab ta yi wannan jawabi ne a gaban Kwamitin Majalisar Tarayya na Kasafin Kudade.

Cewa ta yi ta haka ne za a kara samun kudaden shigar tafiyar da ayyukan Kasafin 2019.

Ministar ta ce an karkasa hanyoyin samun kudaden harajin zuwa gida uku, wadanda ta roki Majalisar Tarayya da su daure su bada goyon bayan shigo da sabbin hanyoyin da za a karbi harajin ga ‘yan Najeriya.

Ta ce hanya ta farko it ace jajircewa da kuma tabbatar da an ci gaba da karbar haraji a inda duk ake ci gaba da karba a yanzu.

A wannan mataki ne Zainab ta ce gwamnatin tarayya ta dauki tsauraran matakin toshe duk wata kofar da harajin da ya kamata a karba ba ya shiga aljihun gwamnati.

Sannan kuma akwai matakin hada kai da guiwa da masu zuba jari domin samar da kudaden da za a yi ayyukan makamashi da su.

“Hanya ta biyu kuma ita bijiro da sabbin hanyoyin da za a karbi kudaden haraji tare da tilasta wa wanda duk bai biya ya tabbatar cewa ya biya.

“Ina shaida wa Kwamitin Majalisar Tarayya cewa mun tsara hanyoyin bijiro da samun kudaden shiga ga gwamnati, ta hanyar kara hanyoyin karbar kudaden haraji, wadanda nan gaba kadan za mu dawo majalisa domin mu zauna tare da ku mu tattauna su. Haka kuma za mu kara harajin ‘VAT’’.

Harajin ‘VAT’ dai shi ne harajin jiki-magayi, wanda ake tatsar karin kashi 5 bisa 100 daga hannun kwastoma na adadin kudin kayan da ya saya. Shi ne aka ce za a kara zuwa kashi 7.5 bisa 100.

PREMIUM TIMES HAUSA a cikin makon da ya gabata, ta bada labarin Ministan Kasafin Kudi da Tsare-tsare, Udo Udoma, ya ce za a kara yawan harajin jiki-magayi, wanda aka fi sani da ‘VAT’.

Shi ma Shugaban Hukumar Tara Kudaden Shiga na Cikin Gida (FIRS), Babatunde Fowler ya tabbatar da karin kudin ‘VAT’ din tun ma kafin Minista Udoma ya yi bayani.

Sai dai shi Udoma cewa ya yi za a yi karin harajin jiki-magayi ne domin a samu kudin da za a rika biyan karin mafi kankantar albashi da aka yi wa ma’aikta, daga naira 18,000 zuwa naira 30,000.

Share.

game da Author