Ministan Harkokin Ilmi, Adamu Adamu, ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba Najeriya za ta fara amfani da tsarin gurfanar da iyayen da ba su saka yaran su makaranta a kotu.
Adamu Adamu ya ce gwamnatin tarayya za ta dauki kin saka yaro makaranta da wasu iyaye ke yi a matsayin babban laifi.
Ministan ya yi wannan gargadi ne a jiya Litinin, lokacin da ya ke jawabi ga manema labarai yayin taron ganawa da su ta 9 da ma’aikatar sa ta gudanar.
Ya ce duk wani ko wasu iyayen kananan yara da ba su tura su makaranta ba, za a dauki wannan dabi’a a matsayin yi wa gwamnatin tarayya kafar-ungulu a kokarin da ta ke yi wajen ganin ta matukar rage yara masu gagaramba a kan titi ba su zuwa makaranta.
Daga nan sai ya ce ba tare da wata-wata ba kuma za a fara gurfanar da su a gaban kotu, a matsayin wadanda za a ladabtar daga babban laifin da suka aikata.
“Idan ba a dauki kin saka yara makaranta a matsayin wani babban laifi ba, har aka fara kulle iyaye a kurkuku, to matsalar ambaliyar kananan yara masu gagaramba kan titi ba za ta iya rabuwa da mu ba.
Adamu ya ce akwai masu fakewa da al’ada ko addini su ki saka yaran su makaranta.
Ya ce daga yanzu gwamnati za ta dauki duk wani da ya ki saka yaran sa a makaranta, a matsayin wanda ya aikata babban laifi.