‘YAN UBANCI: Gambo ya datse kan dan uwan sa Haladu da adda a Badakoshi

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta bayyana yadda wani matashi mai suna Gambo Sa’idu mai shekaru 22 ya fille kan wansa Haladu Sa’idu mai shekaru 40 da suke ‘yan uba dashi da adda.

Kakakin rundunar ‘yan sanda Audu Jinjiri ya fadi haka wa PREMIUM TIMES inda ya kara da cewa wannan abin takaici ya faru ne ranan Talata da misalin karfe 2:45 na rana a kauyen Badakoshi dake karamar hukumar Gwaram.

” Mun zo mun iske Gambo tsaye akan gawan Haladu rike da addan da ya datse masa kai gangan jikin a gefe

Mazaunan kauyen da suka tattauna da rundunar ‘yan sandan sun bayyana cewa akwai yiwuwar kishin abin hannun Haladu ne ya ingiza Gambo aikata wannan mummunar aiki.

Wasu makusantan su sun bayyana cewa wadannan yan uwa sun dade suna gaba da juna kuma iyayen su basu yi wani kokarin shirya su ba.

Jinjiri yace a yanzu dai Gambo na nan tsare a ofishin su sannan rundunar za ta aika da shi fannin da ake gurfanar da masu aikata laifuka irin haka dake Dutse domin ci gaba da bincike.

Share.

game da Author