‘Yan sanda sun kama Abubakar da ya yi garkuwa da Aisha yar shekara biyar a garin Lafia

0

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa Frank Mba ya bayyana cewa ‘yan sanda sun ceto wata ‘yar shekara biyar mai suna Aisha Ibrahim daga hannun wasu masu garkuwa da mutane a Lafia.

Mba ya ce binciken da suka gudanar ya nuna cewa wani abokin mahaifin Aisha mai suna Abdullahi Abubakar mai shekaru 30 ya sace Aisha a jihar Delta ne sannan ya kawo ta jihar Nasarawa.

” Abubakar ya fadi cewa ya kama Aisha ne yayin da take hanyar zuwa makaranta a ranar 16 ga watan Maris.

” Bayan ya dauke Aisha sai Abubakar ya kai ta wajen mahaifiyarsa Jummai mai shekaru 62 a lafia da take taya shi ajiye yaran da yake sacewa sannan ya tuntubi iyayen Aisha su biya kudin fansa kafin ya sake ta.

Ya ce rundunar za ta ci gaba da gudanar da bincike amma kuma tuni har an mika Aisha ga iyayenta.

Mba yace sun kama Abubakar tare da mahaifiyarsa Jummai kuma suna farautar wani Inusah Ibrahim mai shekaru 58 da ya taya Abubakar sace Aisha.

Share.

game da Author