‘Yan sanda sun fi ma’aikatan kowace hukuma lalacewa wajen tafka cuwa-cuwa –Bincike

0

Wani sabon bincke na baya-bayan nan da aka gudanar kuma aka fitar a yau Alhamis, ya fallasa irin yadda jami’an ‘yan sandan Najeriya suka ciri tutar farko wajen ira kitsa tuggun cuwa-cuwa da harkallar cin hanci da rashawa.

Kungiyar nan mai bin diddigin ganin an gudanar ayyuka a bisa ka’ida, gaskiya kuma bisa turbar da ta dace, wato SERAP, ita ce ta fitar da bayanin binciken.

SERAP ta ce ‘yan sanda sun yi wa sauran hukumomi da ma’aikatu zarra da rata mai tazarar gaske, wajen bata sunan su idan ana maganar hukumomin da suka bata sunan su kuma suka damalmala jikin su da dagwalon kwatamin kazantar cuwa-cuwa, rashawa da cin hanci.

Har ila yau, SERAP ta ce Ma’aikatar Samar da Hasken Lantarki ko Makamashi ce lamba biyu, wadda ke biye da ‘yan sanda wajen baci da almundahana.

Sauran hukumomin da ‘yan Najeriya suka ce su ma su na da dimbin lalatattun ma’aikata, sun hada da Ma’aikatar Shari’a, Ma’aikatar Ilmi, Ma’aikatar Lafiya.

Kashi 70 bisa 100 na wadanda aka tamabaya ne suka bada wannan fatawar maciya hanci, rashawa da almundahanar.

Sannan kuma wannan bincike ya kara nuna cewa irin yadda ake wawurar kudaden gwamnati daga shekaru biyar zuwa yau, bai canja zani ba. Ma’ana, jiya kamar yau kenan.

Wannan sabon rahoton da SERAP ta fitar da shi ne kuma aka kaddamar da shi a Otal din Sheraton, Lagos a yau Talata.

Binciken ya nuna cewa, “Cikin mutane 100 da suka yi kowace irin mu’amala da ‘yan sanda, to 54 ba su wanyewa salum-alum, sai sun bada kudi.

“Kai ana ma da kwakkwaran hasashen cewa mutane 63 bisa 100 idan suka yi mu’amala da ‘yan sanda, sai an karbi cin haci a hannun su. Wasu ma na ganin kashi biyu bisa uku na duk wanda ya yi mu’amala da ‘yan sanda, to sai ya biya su cin hanci.”

Akin Oyebode, wanda shi ne shugaban taron kaddamar da rahoton, ya ce “Ana yi wa Najeriya kallon uwar Afrika. Amma abin takaici wannan uwa ba ta ma iya ko da shirya sahihin zabe wanda jama’ar kasa da duniya za ta amince da sahihancin sa. Wannan ya na bata wa Najeriya suna, kuma ya yi wa kasar babban tabo a fuska wand aba a san lokacin da a iya kankare shi daga fuskar ba.”

Ya kara da yin dogon sharhi wajen neman mafita, tare da kara jan hankalin nuna wa jama’a cewa ‘yan siyasa ma su na tatse dukiyar kasar nan ta hanyar wawure dukiyar al’umma.

Wannan kuwa inji shi, sata ce tuburan ake mata kinaya ana kiran ta wawura.

Share.

game da Author