‘Yan jagaliya sun sace akwatunan zabe a jihar Kogi

0

Wasu ‘yan jagaliyar siyasa dauke da bindigogi sun sace akwatunan zabe a rumfunar zabe dake unguwannin Adankolo, Lokoja jihar Kogi.

Wadannan yan jagaliyar sun sace na’urar ‘Card Reader’, takardun dangwala zabe, akwatunan zabe da wasu kayayyaki a wadannan rumfunar zabe.

‘Yan jagaliyar sun saci kayan zabe a rumfunar zabe biyar dake makarantar firamaren St Luke dake Adankolo,rumfar zaben dake NEPA a Lokoja, rumfar zabe dake mazabar A da rumfar zabe dake Okengwe a karamar hukumar Okene.

Dama can mazaunan jihar da wani dan takarar kujeran majalisar dokoki na jam’iyyar PDP Suleiman Babadoko sun koka game da alamun tashin hankalin da suke ganin zai iya aukuwa a lokacin zaben.

A dalilin haka Babadoko ya yi kira ga jami’an tsaro na SSS da su gaggauta daukan mataki game da abin da ya faru.

Share.

game da Author