ZABEN GWAMNONI: ’Yan jagaliya sun babbake firamare da dukkan kayan zaben da ke ciki a Jihar Benuwai

0

PREMIUM TIMES ta tabbatar da cewa an babbake dukkan kayan zaben da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta tanadar kafin ta raba a RCM Primary Aya.

An banka wutar ce a Karamar Hukumar Gwer ta Gabas da ke jihar Benuwai.

Kayan an tanadar da su ne domin aikin zaben da za a gudanar a Mazabar Mbolom.

Ganau wanda ya ga lokacin da aka banka wutar, ya shaida wa wakilin NAN cewa kafin ‘yan bindigar su cunna wutar, sai da suka yi harbi a sama, kowa ya dafe keya ya arce, sannan suka banka wa makarantar da kayan zaben wuta.

Jami’in Zabe na yankin, Ngunan Yongo ya tabbatar da an banka wutar da wakilinmu ta wayar tarho.

An kone kayan ne kafin a kai ga fara rarraba su domin zaben gwamna da na majalisar dokoki da za a gudanar yau Asabar.

Share.

game da Author