Wasu ’yan bindiga sun bude wuta yayin da ake tsakiyar gangamin yakin neman zaben jam’iyyar APC a kan titin Edet Akpan, Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom.
An tabbatar da ji wa da dama rauni a wurin.
Wani mai babur din A Daidaita Sahu ya ce da idon sa ya ga lokacin da wata mota kirar Toyota Hilux ta tsaya a tsallaken titi, inda wasu mutane suka fito daga cikin motar, suka tsallaka suka tsaya a bakin kofar shiga filin taron.
Ya ce su ne suka bude wuta cikin taron, kuma suka yi sauri, suka tsallaka titi a guje, suka shiga motar su suka arce.
Filin kamfen din dai babba ne, ya nunka filin kwallo fadi, kuma a wurin ne ake yawan taruruka na siyasa. A kullum wurin ba ya rabo da jama’a tun da kakar yakin neman zabe ta shigo.
Ko a ranar Litinin sai da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya halarci taron APC a wurin, inda ya wakilci shugaba Muhammadu Buhari.
APC dai ta zargi PDP da laifin kai harin. Ita kuma PDP ta nesanta kanta daga harin da aka kai wa APC a filin kamfen din.
Kakakin ‘yan sandan jihar Akwa Ibom da PREMIUM TIMES ta kira bai dauka ba, har yanzu bai kira ko ya rubuto sakon tes ta waya ba.