Yadda ‘Yan Bindiga Suka Kashe ’Yan Sintiri 17 a Birnin Gwari, jihar Kaduna

0

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna ta bayyana cewa an ‘yan bindiga sun kashe akalla ‘yan banga 17 a kauyen Jan Ruwa da ke cikin Karamar Hukumar Birnin Gwari, Jihar Kaduna

Kakakin rundunar Yakubu Sabo, ya ce jami’an su sun samu rahoton wannan mummunan kisa ne cewa a ranar 12 Ga Maris, wajen karfe 11:45, wasu mahara sun shiga kauyen Jan Ruwa sun yi awon gaba da shanu.

“Ana cikin haka sai wani gungun ‘yan sintiri da ke kauyen, wadanda sun je sintiri a dajin Zamfara, su na kan hanyar komawa gida Jan Ruwa, suka samu labari, sai suka bi barayin shanun.

“Sun bi barayin a cikin jeji, aka yi barin wuta sosai da bindigogi har aka kashe ‘yan sintiri da dama.”

Sabo ya ce jami’an ‘yan sanda da suka hada da mobal da ‘yan sintiri sun kai dauki inda suka tsinto gawarwaki 15 daga baya kuma an ce an kara samun wasu gawarwaki biyu.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Kaduna Ahmad Abdurrahaman ya yi tir da kisan kuma ya nuna alhini da ta’aziyya.

Sannan kuma ya sha alwashin kamo maharan domin su fuskanci hukuncin abin da suka aikata.

Ya roki jama’a masu masaniya a kan mahara da su rika sanar da jami’an tsaro.

Share.

game da Author