Yadda wani zautacce ya guntule hannun makwauciyar sa da adda

0

Wani ibtila’i ya faru a cikin dare a garin Omu-Aran da ke Jihar Kwara, inda a ranar Asabar wani birkila mai suna Lukman ya kafta wa makwauciyar sa sara da adda a hannu, har hannun ya guntule.

Muibat wadda tsautsayin ya sama, gyatuma ce mai shekaru 60, ya gutsire mata hannu ne bayan da ya rigaya ya sassari wasu da suke zaman haya tare a gida daya su biyu.

Al’amarin ya afku ne a unguwar Orolodo, bayan fadar basarake Olomu a cikin Omu-Aran.

Tsohuwar da aka cire wa hannun dai matar aure ce, kuma an garzaya da ita asibitin Ajisafe, su kuma mutane biyu da ya fara sara da adda, aka garzaya da su Babban Asibitin Omu-Aran.

Ko da wakilin NAN ya isa asibitin domin gane wa idon sa wadda aka ji wa ciwon, an ce masa a lokacin da ya je ba a shiga duba maras lafiya, har sai karfe shida na yamma.

An shaida masa cewa an rigaya an yi mata aiki a hannun, ba ta da sukunin ganin masu dubiya, har bayan karfe 6 na yadda.

Sai dai kuma an shaida masa cewa ba ta cikin wata gigita kuma jikin ta na karbar magani da aikin da aka yi mata.

Haka wata jami’ar jiyya ta shaida wa wakilin, amma ta ce kada ya bayyana sunan ta.

Daya daga cikin ’ya’yan wadda aka cire wa hannun mai suna Azeez Abifarin, ya ce aika-aikar ta faru wajen karfe 10 na dare.
Ya ce a lokacin har ma sun yi shirin kwantawa barci.

“Farkon abin dai sabani ne ya shiga tsakanin yaya na Abeeb da kuma Lukman a kan wata mushen akuya da shi Lukman ya kinkimo ya na gasawa.
Abeeb ya yi masa magana sai kawai ya dauki adda ya yi ta kaftar sa.

“To ganin Abeeb a cikin jini ga rauni a jikin sa ne ya tayar da hankalin maman mu, ta tafi ta tunkari Lukman. A nan ma ya daga adda ya kafta mata sara a hannu, har hannun ya cire.

“A kai ya yi niyyar sarar ta, amma sai ta daga hannun ta na hagu ta tare, shi ne ya samu hannun na ta.”

Shi kuma mahaifin wanda ya yi saran, ya hadu da wakilinmu a asibitin da ya je ganin Muibat, ya ce ta na samun sauki.

“Hankali na ya tashi matuka a lokacin da na ga irin raunin da ya yi musu. Lukman ya je gida ya same ni kwana daya kafin abin ya afku.

Bai nuna a zuciyzar sa akwai wata nifaka a kan wani, ko wani alamun ya na da niyyar aikata wata mummunar ta’asa ba.”Inji mahaifin sa.

An dai damke Lukman tun a cikin daren da ya yi aika-aikar, aka kulle shi a ofishin ‘yan sanda na Omu-Aran.

Share.

game da Author