Yadda wani ya tuma tsalle daga Ibadan ya ‘dira lahira’

0

Wani mutum da aka yi zaton zautacce ne, ya tuma tsallen da ya yi sanadiyyar ajalin sa a unguwar Sango, cikin Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.

Wadanda aka yi abin a kan idon su, sun tabbatar da cewa mutumin ya tube tsirara ne, sannan ya kutsa kai cikin harabar ginin Wema Bank da ke Sango.

An ce ya shiga ne ta wata karamar kofa, inda kai-tsaye ya zarce ya hau dogon karfen da aka kafa na’urorin sadarwa.

Shi ma Kakakin Yada Labarai na ’Yan Sandan Jihar Oyo, mai suna Fabeyi, ya ce jami’an da ke tsaron bankin, ba su farga da shi ba, sai bayan da ya hau kololuwar saman karfen.

An yi gaggawar kiran jami’an kashe gobara, amma kafin su karaso, sai zautaccen ya diro daga sama, ya subuto a kan rufin kwanon ginin bankin.

“Karfin faduwar sa da nauyin sa, sai da ya sa rufin kwanon ya barke, har mutumin ya barka sili, sannan ya fada cikin bankin, a kasa.

“Daga nan an kira wani jami’in bankin domin ya gaggauta zuwa ya bude kofar bankin.

“Yayin da aka shiga cikin bankin aka same shi, an ga jini na ta zuba daga bakin sa. Daga nan aka garzaya da shi Asibitin Jami’ar Ibadan, inda su na zuwa likita ya tabbatar musu cewa ya rasu.” Inji Fadeyi.

Ya ce a halin yanzu an ajiye gawar sa a Asibitin Adeoyu, kafin a gano ko wane ne, sannan a gano dangin sa.

Share.

game da Author