Yadda wani Likiti a Sokoto ya dirka wa matan wani maganin barci yayi lalata da ita

0

Allah ya tona asirin wani likita a wani asibiti da dake Sokoto inda ake tuhumar sa da dirka wa wata matan Aure maganin barci sannan ya Yi lalata da ita.

Kamar yadda mijin wannan mata ya shaida wa jaridar Daily Nigerian, ya ce matar sa ce ta fadi masa abin da ya faru bayan ta kagara danne abin a zuciyar ta.

” Matata ce ta fadi mani abinda ya faru inda tace, bayan ta tafi asibitin wajen likitan kamar yadda ya umarta sai ya ce zai yi mata allura bisa ga wani aikin kaban ciki da aka yi mata a baya. Bayan ta farka daga barcin wannan allurar da likita Tijjani Faruk yayi mata sai ta ganta ba yadda ta zo asibitin ba.

” Daga nan sai ta ce masa Kai ko likita me yasa ka aikata wannan wannan mummunar aiki akaina. Da bude bakin sa sai ya ce ta yi hakuri sha’awarta ne ya kaita ga haka.

Daga nan sai mijin ya ce mata ta koma ta sake Yi masa magana kan abin da ya faru a tsakanin su cewa za ta gaya wa mijin ta. Amma Kuma ta tabbata ta dauki hirar su da ta waya a boye.

Wannan mata ta ko aikata hakan, ta kunna wayarta bai sani ba sannan ta ce masa ita fa abin da ya faru a tsakanin su ya na tada mata hankali zata fadi wa mijin ta.

Haka fa shi gogan naka ya rika maimaita abubuwan da suka faru a tsakanin su ita Kuma tana ta dauka.

Mijin wannan baiwar Allah ya sanar wa ma’aikatar lafiya ta jihar sannan Kuma da kungiyoyin da ke kula da ayyukan likitoci ta kasa.

Da aka nemi ji daga bakin wannan bawan likita da farko ya karyata hakan sai dai bayan sauraran hiran su da yayi da wannan mata sai ya ce ay ba saduwa da ita yayi ba domin basu kai ga shiga juna ba.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa har yanzu ana ci gaba da bincike game da wannan ta’asa da likita
Tijjan Faruk ya aikata.

Share.

game da Author