Yadda sojoji da ’yan jagaliya suka hargitsa sakamakon zabe a jihar Ribas – INEC

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta dora laifin hargitsa tattara zaben Jihar Ribas a kan wasu sojoji da kuma ‘yan jagaliyar siyasa.

INEC ta ce su ma ‘yan jagaliyar sun yi amfani da makamai wajen tayar da hargitsinn da tilas INEC ta dakatar da aikin tattara sakamakon zaben jihar.

INEC ta ce sojojin da kuma ‘yan dabar siyasa sun yi kokarin yi wa jama’a fashin abin da suka zaba a Jihar Ribas.

A cikin wata sanarwa da INEC ta fitar ranar Asabar da safe, ta ce za ta yi amfani da rahoton da kwamitin binciken abin da ya faru a jihar Ribas ya kawo mata.

Kwamitin wanda ke karkashin An thonia Okoosi-Simbine, ya rigaya zauna a ranakun Litinin da Talata. Kuma ya yi wa jami’an INEC na Kananan Hukumomi da Jiha, Jami’an tsaro da ma’aikatan wucin-gari na NYSC da wakilan jam’iyyu tambayoyi.

Kakakin INEC Festus Okoye ya bayyana cewa:

“INEC ta nuna rashin jin dadin yadda sojoji da ‘yan bangar siyasa dauke da makamai suka hargitsa tsarin tattara sakamakon zaben da jama’a suka zabar wa kan su.”

“Sojoji da ‘yan jagaliyar siyasa dauke da muggan makamai sun rika mamaye cibiyoyin tattara zabe, ta yadda suka razanawa da firgita jama’a tare da kakkame jama’a ba gaira ba dalili. Ta haka suka hargitsa aikin tattara zaben.

INEC ta ce sakamakon Kananan Hukumomi 17 daga cikin 23 duk ya na hannun ta.

Ta ce za a gaggauta kammala aikin tattara sauran sakamon da ya rage.

Share.

game da Author