Wasu ma’aikatan wucin gadi na INEC a Cibiyar Zabe ta Babbar Sakandaren Ikosi-Ketu da ke Kosafe a Lagos, sun rukume gardamar rabon kudin da wani dan siyasa ya raba a yau Asabar.
An yi zargin cewa jagoran APC ne Bola Tinubu ya raba musu kudin.
Amma PREMIUM TIMES ta kasa samun tantance gaskiyar lamarin daga Tinubu.
Sun yi boren cewa idan ba a raba kudin da sub a, to su ma ba za su yi aikin zaben ba.
Sun ce sai an bas u na su kason sannan za su kwashi kayan zabe su tafi runfunan zabe da aka tura su.
Wani jami’in zabe ya shaida cewa an kai kudin ne yau Asabar, amma sun ki raba su.
Yayin da wani jami’in INEC ke lallashin su, ya ce za a ba kowane naira 10,000.00.
Sai dai kuma ma’aikatan na wucin gadi sun ce ba za su karbi naira 10,000.00 kowanen su ba.
Yayin da wasu ke cewa sai an ba kowa naira 40,0000, wasu kuma sun tsaya kan cewa za su karbi naira 20,0000.
“An ba Ogudu naira 10,000 ya karba. To ni dai ba Ogudu ba ne. Nan Ikosi ne, idan ba a biya mu na mu kason ba, to ba za mu yi aikin zben ba.” Inji daya daga cikin jami’an.