Gwamnan jihar Zamfara mai bari gado AbdulAziz Yari ya bayyana cewa amincewa da yadda yake shugabantar mutanen jihar Zamfara ne ya sa jama’an jihar suka yi wa jam’iyyar APC goma ta Arziki suka fito kwansu da kwarkwata suka zabe ta a zaben gwamna da ya gabata.
Yari ya bayayyana haka ne da ya ke zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa.
” Da yawa an yi ta yin korafi cewa wai na tare a Abuja bana zuwa jiha ta domin duba halin da mutane ke ciki. Abin da basu sani ba a kullum ina tare da mutane na a jihar Zamfara kuma tabbas sun shaida irin romon dimokradiyya da muka rika kwararo musus a duk fadin jihar.
” A dalilin haka ne ya suka saka mana, suka fito suka zabe mu gaba dayan su.
” Na san yadda jihar Zamfara take, tuna 1999 na ke siyasa a jihar. Na san kowa kuma na san komai. Duka da matsalar da muka samu a tsakanin mu ‘yan siyasa. Na koma kowa na bishi mun sasanta a tsakanin mu. Shine ya sa kuka ga cikin kwanaki biyu kacal jam’iyyar ta yi nasara a zaben gwamna na jihar.
” Ba ya ga kokarin taimakawa mutanen jihar da muka yi, shugaba Buhari ya nuna wa mutanen jihar cewa yana tare da su kuma yana iya kokarin sa wajen ganin an kawo karshin ayyukan ‘yan ta’adda da ya gallabi mutanen jihar.
Discussion about this post