Matar Suleiman Abubakar, Shugaban Kungiyar Wakilan Kafafen Yada Labarai na Jihar Nasarawa ta samu kubuta, tare da sauran mata uku da aka yi garkuwa da su.
An dai yi garkuwa da su ne cikin makon da ya gabata, a kan hanyar su ta komawa Lafiya, daga Keffi. An tare su a tsakanin Gudi da Keffi.
Kakakin Yada Labarai na Rundunar ’Yan Sandan Nasarawa, Smaila Usman, ya tabbatar wa manema labarai jiya Juma’a a Lafiya cewa masu garkuwar sunn sako matan misalin 9:45 na dare a ranar Alhamis.
Usman ya ce masu garkuwar sun saki matan ne saboda matsin lambar bincike da neman su da jami’an tsaro suka rika yi.
Hakan ce ta sa suka sake su, domin sun fahimci kun kusa kure musu gudu.
Ya ce dukkan matar da aka kamac din, sun je yin rajistar aikin bautar kasa ne a sansanin NYSC da ke Keffi, Jihar Nasarawa.
Ya ce tuni kowace ta koma gida cikin iyalan ta.
Sai dai shi kuma Shugaban Kungiyar ’Yan Jaridun, ya shaida wa NAN cewa sai da ya biya kudi kafin a saki matar sa.
Ya ce masu garkuwar sun kira shi ta lambar wayar matar sa, suka ce ya je ya kai kudi a daidai wani wuri, a kan hanyar dai da aka yi garkuwar da su matan.
Abubakar ya ce, “Na kai kudin a daidai inda suka umarce ni. Sannan suka ce na je can wajen kauyen Mandara domin na dauki mata ta.”
Ya gode wa Allah da ya tserar da matar ta sa.
An dai yi garkuwa da matar ce a kan hanyar su ta komawa Lafiya daga Keffi.
Abubakar ya ce bayan da aka tare su, shi ya samu tserewa, amma sai aka kama matar sa da wadancan sauran mata uku.