Yadda aka dagula tsarin tattara sakamakon zabe a mazabu – CCD

0

Cibiyar Inganta Tsarin Dimokradiyya (CCD), ta yi ikirarin cewa an dagula tsarin tattara sakamakon zaben shugaban kasa da na majalisar dattawa da ta tarayya a cibiyoyin tattara sakamakon zabe a mazabu.

CCD, wadda ta yi aikin sa-ido kan zabe tare da PREMIUM TIMES da PLAC, ta tabbatar da cewa a rahotannin da ta tattara daga jami’an ta da ta tura rumfunan zabe 8,809 a cikin jihohi 36 na kasar nan da Abuja, sun bada rahotannin cewa an damalmala lissafin tattara sakamakon zabe a mazabun kasar nan.

Sun ruwaito matsalar “kauce wa ka’ida, rashin kwarewar aiki daga wasu ma’aikatan wucin-gadi na INEC, matsalar tsaro, yadda jami’an tsaro suka rika yi wa jami’an INEC barazana, harigidon ‘yan jagaliya da ‘yan bangar siyasa da na ejan na jam’iyya da kuma hana ‘yan jarida da masu sa-ido damar gane wa idon su wainar da ake toyawa.”

A cikin wannan rahoto da CCD ta bayyana ranar Litinin, ya ce baya ga tura masu sa-ido masu dimbin yawa da ta yi, ta kuma yi amfani da wata manhajar tattara bayanai da ta rada wa suna “Zabe SR”, wadda ke samar da bayanai na yadda zabuka ke gudana daga rumfunan zabe da cibiyoyin tattara sakamakon zabe.

CCD ta ce aikin tattara sakamakon zabe abu ne mai muhimmancin da yin sako-sako da shi ka iya kara wa zabe inganci ko kuma rage masa sahihanci.

Rahoton ya kara da cewa duk da akwai sharudda da ka’idojin da dokar zabe ta gindaya kan yadda za a tattara sakamakon zabe, tun daga matakin mazabu har zuwa na kasa baki daya, INEC ta sha fama wajen tattara bayanan.

An fitar da wadannan ka’idoji ne tun a ranar 12 Ga Janairu, 2019.

Matsalar farko da INEC ta fara fuskanta a wajen tattara sakamakon zabe, ita ce matsalar sufuri. CCT ta buga misali da jihar Enugu, inda ta bayyana cewa an rika shan wahalar tattara sakamakon zabe daga rumfunan zabe saboda matsalar rashin wadatattun ababen hawa.

Sannan kuma a Jihar Enugu din dai da kuma Jihar Abia, tattara sakamakon zaben ya zo da cikas, domin a wasu wuraren INEC ba ta bayyana ainihin cibiyoyin da za a tattara bayanan ba.

HARKALLA DA MATSALAR RASHIN IYA AIKI

CCD a cikin rahoton ta, ta ce an samu cikas wajen tattara bayanai inda wasu jami’an INEC na wucin-gadi suka rika aikata ba daidai ba, sannan kuma wasun su ba su da cikakkar masaniya ko kwarewar yadda ake gudanar da aikin tattara sakamakon zaben.

“Saboda harkallar da wasun su suka rika yi, da kuma wasun su da dam aba su ma iya lissafin hada adadin kuri’u ba, sun rika tabka kuskure a cikin takardun rattaba sakamakon zabe. An rika cin karo da wuraren da adadin kuri’un da aka tattara sun sha bamban da sakamakon da ke a rubuce. To wadannan sun taru sun kara haifar da latti ko jan-kafa wajen tattara sakamakon zabe.”

JIHAR KADUNA

“A jihar Kaduna kuwa, aikin tattara sakamakon zabe ya samu cikas saboda ba a kai kayan aikin zabe a wurare da dama. Sannan kuma wasu Jami’an Zabe ba su san aikin su ba.

Jami’an CCD da ke sa-ido sun tabbatar da cewa Gwamna Nasir El-Rufai ya koma rumfar zaben sa da misalin karfe 6 na yamma domin ya ga yadda ake kidayar kuri’u. Yayin da ya fice daga wajen da karfe 9:30 na dare a fusace, jami’in zabe na ta kikiniyar tantance ainihin adadin wasu kuri’u.

“Baya ga kura-kuran da aka rika tabkawa kuma, an samu wuraren da aka tabka cuwa-cuwa a bangaren ma’aikatan wucin gadi na INEC a lokacin da ake tattara sakamakon zabe. Misali, a Mazabar Badarawa, Kaduna ta Arewa, an ruwaito cewa jami’an wucin gadi na INEC guda uku suka arce da takardun rubuta sakamakon zabe.

Sakamakon zaben wannan mazaba bai isa cibiyar tattara sakamakon zabe na Karamar Hukuma ba, har sai bayan sa’o’i 48 da kammala zabe.

CCD ta ci gaba da buga dimbin misalai a Jihar Bauchi, Lagos, Rivers da Jihar Delta, akasari wadanda suka shafi harkalla da kuma matsalar tsaro da barazana da kuma wuraren da aka hana ‘yan jarida da masu sa-ido shiga su ga wainar da ake toyawa a lokacin tattara sakamakon zaben.

Ta kuma bayyana wuraren da aka yi amfani da ‘yan sanda wajen gadin cibiyoyin tattara sakamakon zabe domin su hana duk wani dan gaji-ganin shiga ganin abin da ke faruwa

DAGA BAKIN CCD

“Aikin tattara sakamakon zabe tun daga matakin mazabu ya ci karo da kalubale mai yawa a fadin kasar nan. Amma dai Jihar Legas da Ogun ne aka samu kashi 22 bisa 100 na rahotannin matsalolin da aka fuskanta. Sokoto kashi 9 bisa 100. Rivers kashi 8 bisa 100, Kaduna kashi 7 bisa 100.

“Matsalolin da aka samu a jihar Rivers duk ‘yan sara-suka ne da jami’an tsaro suka haddasa su. Wannan kuwa ya na da nasaba ne daga rigingimun siyasar da suka dabaibaye manyan ‘yan siyasar jihar a tsawon shekaru masu yawa.

A karshe CCD ta ce idan ba a magance matsalar dagula tsarin tattara sakamakon zabe daga mazabu tun kafin zaben ranar Asabar mai zuwa ba, to za a fuskanci karancin masu jefa kuri’a a zaben gwamna. Sannan kuma bayan kammala zabe za a sha fama da sauraren kararraki daga wadanda aka yi wa rashin adalci a wajen tattara sakamakon zabe.

Daga nan sai CCD ta shawarcin INEC ta dukufa wajen kara bai wa ma’aikatan ta na wucin-gadi horon da ya dace kuma ta tabbatar da an hukunta dukkan wadanda ke da hannu wajen aikata ba daidai ba.

Ta kuma yi kira ga kafafen yada labarai da kungiyoyi su ci gaba da matsawa domin tabbatar da samun ingantacciyar dimokradiyya.

Sannan kuma ta yi kira ga jami’an tsaro da su daina wuce-gona-da-iri.

Share.

game da Author