Yadda aka ceto Alaramma Ahmad Sulaiman

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta sanar cewa ta ceto Alaramma, Ahmed suleiman da aka yi garkuwa da a Katsina.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Isah Gambo ne ya sanar da haka cewa an ceto alaramman ne tare da wasu 5 da aka yi garkuwa da su.

” An sako Alaramma Ahmad ne da misalin karfe 4 na Asuban Laraba. Sannan kuma ina so in tabbatar muke da cewa ba a biya kudin diyya ba.

Kamar yadda Jaridar PR ta wallafa, wata muryar daya daga cikin maharan da suka kama shi da ake ta watsawa a soshiyal midiya, ta nuna yadda ake tattauna batun sakin na sa da wani da ya ce ya na magana ne a madadin iyalan malamin.

Baya ga shaharar da Sheikh Ahmad Sulaiman ya yi wajen karatu a wa’azin kungiyar Izala bangaren Kaduna, sannan kuma ya yi suna a zaben 2019, inda ya rika sheka addu’o’i a kan Shugaba Buhari na APC ya samu nasarar lashe zabe a kan abokin takarar sa, Atiku Abubakar na PDP.

Daya daga cikin wadanda suka yi garkuwa da malamin ya ce su ba garkuwa da shi suka yi niyyar yi tun da farko ba.

Ya ce kwangilar kashe shi aka ba su, kuma sai da aka ba su naira milyan 300 kafin su tare shi a kan hanya su kama shi.

Ya ce tun daga Kebbi su ke bin sa. Wani babban dan siyasa ne ya ba su kudi domin su kashe shi.

Dan bindigar ya ce an shaida musu cewa Ahmad Sulaiman dan ta’adda ne, don haka su kashe shi.

Amma yayin da suka kama shi, sun fahimci ba dan ta’adda ba ne, shi ya sa ba su kashe shi ba.

Daga nan sai ya ce abin da suke so, kawai a biya su naira milyan 300 da suka karba daga hannun wanda ya ba su aikin kashe malamin, sai su maida masa abin sa. Ya ce tunda ba su kashe malamin ba, to tilas su maida kudi ga wanda ya ba su kudi domin su kashe shi.

Share.

game da Author