Ya Allah Kayi Muna Maganin Matsalolin Da Suke Addabar Mu, Daga Imam Murtadha Gusau

0

Bismillahir Rahmanir Rahim

Allahummah Ya Muqallibal Qulubi Thabbit Qulubana ala diynika. Ya Hayyu Ya Qayyumu. Ya Samiy’u Ya Basiyru, Ya Haadi Ya Salamu, Ya Saatiru Ya Sattaaru, Ya Zal Jalali Wal Ikraam. Ya Rabbi! Ya Rabbi!! Ya Rabbi!!!

Ya Allah muna gode maKa saboda ni’imomin da Ka zuba a gare mu. Muna godiya gareKa Akan kariyar da Kake ba wannan Al’ummah tamu Duk da gafala, da dimuwa da gigita da hargitsi da hayaniya da ta Sami kanta a ciki.

Ya Allah muna gode maka da Ka sanya mu cikin al’ummah ta GASKIYA, mai Amana kuma mai tarbiyyah. Al’ummar da ko makiyanta sun shaida cewa ba asharariya ba ce, ba almubazzariya ba ce, kuma cikakkiyar mai kishin kan ta ce, mai Kaunar addinin ta ce. Ya Ubangiji, Kai shaida ne Akan halin da wannan al’ummah take ciki na barazana, cin amana, Zamba cikin aminci da zagon kasa na rashin tsaro da sauransu. Ya Ubangiji, makiya sun zagaye wannan al’ummah, suna kai hare-hare a jihohin Zamfara, Katsina, Kaduna, Borno, Adamawa, Yobe da wani sashe na Sokoto, suna zubar da jinin bayin ka, suna sace dukiyoyin bayin ka, suna garkuwa da bayin ka domin neman kudin fansa, suna neman hana wadannan al’ummomi KATABUS! Abin yakai LA HAWLA WA KA QUWWATA ILLA BILLAH!

Ya Ubangiji, mu bayinKa ne raunana, masu zunubi, amma masu yawan tuba a gareKa. Ya Allah Ka cece mu daga azzaluman bayinka. Ya Allah bayinKa suna cikin WAHALA, da matsananciyar fatara da yunwa da talauci. Ya Allah Ka kawo mana dauki, Ka lalata duk wani mummunan shiri da miyagu suke yi Akan wannan al’ummah ta mu.

Ya Allah Ka gajiyar da masu yi da wadanda ke daukar nauyinsu. Ya Allah Ka jarrabesu da talauci, da kunci da gajiya da ASARAR da ba ta MISALTUWA! Ya Allah Ka sa duk wani makirci na su ya zama HABAA’AN MANTHURAH. Allah Ka jarrabesu da yunwa Kamar yadda suke saka Mu cikin ta; Ka jarrabesu da talauci Kamar yadda suke sa mu cikin sa. Ya Allah Duk Wanda yake cikin wannan al’ummah kuma yake ha’intarta, Ya Allah Ka tona asirin sa da gaggawa, duniya ta gane ha’incinsa, kuma ayi waje Da shi.

Ya Ubangiji Ka TUMBUKE Duk wani Wanda yake Hana ruwa gudu a cikin wannan kasa ta mu, Ka tozarta shi, Ka wulakantashi. Ya Allah ka ba shugabannin mu da Sarakunan mu da dukkanin jama’ar mu kariya ta musamman daga gare ka. Ya Allah ka hada kan wannan al’ummah a kan gaskiya, manyan ta da talakawan ta. Ya Allah Ka ba sojojin mu da dukkanin jami’an tsaron mu sa’a da kariya. Ka ba su nasara da Daukaka. Duk masu nufin wannan Al’ummah da Sharri, ko a cikin gida suke ko a waje, Ya Allah Ka lalata shirin su, Ka kaskantar da su. Wadanda suke satar dukiyar kasarmu, suke Boyewa a bankunan cikin kasa ko a wajen Nijeriya, ya Allah Ka jarrabesu da talauci-gama-gari, Wanda bai da magani har bayan bayansu.

Ya Allah Ka saka su a kunci Kamar yadda suke kuntata mana. Ya Allah Duk Wanda ba ya tausaya muna, Ya Allah Ka Kuntata masa. Ya Allah ka taimaki dukkanin masu taimakon mu. Ya Allah Dan uwan mu, Alarammah Ahmad Ibrahim Suleiman ka kubutar da shi daga hannun masu garkuwa da shi, ka kare shi daga sharrin su. Ka sada shi da iyalan sa da ‘yan uwansa cikin koshin lafiya. Wadanda suka sace shi idan masu shiryuwa ne, Ya Allah ka shiryar da su. Idan ba masu shiryuwa ba ne, Ya Allah kayi muna maganin su.

Ya Allah rikice-rikicen siyasa da suke addabar kasar nan, ka sa a gama su lafiya, a warware su cikin ruwan sanyi, ba tare da tashin hankali ko zubar da jini ba.

Ya Sami’u, Ya Basiru, Ya Hakamu, Ya Adalu, Ya Mujibud Da’awaati, Ya Mugiithu. Ya Allah Ka Amsa mana wadannan addu’o’in, domin girmamawa da son da muke yiwa ManzonKa Annabi Muhammadu (SAW); domin tsarkin sunayenka, domin alfarmar wannan lokaci, Amin, Thumma Ameen!

Dan uwan ku:

Imam Murtadha Muhammad Gusau, daga Okene, Jahar Kogi, Nigeria. Za’a iya samun sa ta: gusaumurtada@gmail.com ko kuma +2348038289761.

Share.

game da Author