WHO ta kaddamar da na’urar gwaji don kare matsalolin kunne da Ji

0

Domin wayar da kan mutane game da hanyoyin gujewa kurmancewa Kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta kadamar da wata na’uran gwajin yadda mutum ke ji domin kare mutane daga kurmancewa.

WHO ta kaddamar da wannan na’ura ne a taron kare mutane daga matsalolin da za su iya kurmantar da mutum da ake yi ranar uku ga watan Maris ta kowace shekara.

Jami’ar WHO Etienne Krug ta ce mutum zai iya saka wannan na’ura a cikin wayar sa domin amfani da shi a duk lokacin da ya ga dama.

Krug ta ce wadanda suka dara shekaru 60, wadanda ke yawan jin sauti da kara, da wadanda ke aiki da na’urori masu kara na cikin mutanen da ya kamata su yi amfani da wannan na’ura.

Ta ce amfani da na’urar zai taimaka wajen wayar da kan mutane game da kula da kunnuwar su sannan da lokacin da ya kamata su nemi kula domin guje wa kurmancewa za su samu.

Bincike ya nuna cewa mutane miliyan 466 sun kurame a duniya inda daga ciki miliyan 34 yara ne.

Bincike ya kara nuna cewa idan ba a gaggauta daukan mataki ba nan da shekarar 2050 mutane miliyan 900 a duniya za su iya zama kurame sannan samun kulan da ya kamata kuwa zai kara tsada.

Krug ta ce ya zama dole a wayar da kan mutane game da wannan matsala na rasa ji har abada.

WHO ta kuma jero wasu hanyoyi da ya kamata a sani game da wannan matsala

1. Yawan goge kunne da cusa wasu abubuwan da bai kamata ba na iya sa mutum dains jin magana.

2. Mutane da suka dara shekaru 60 na kamuwa da matsalar da ya shafi kunne.

3. Rashin samun maganin kawar da cututtukan dake kama kunne.

4. Yawan jin kara musamman sauti.

5. Yawai ta amfani da magunguna kamar su aspirin, antibiotics, ibuprofen, quinine na kurmantar da mutum.

6. Wadanda suka kurmance za su iya amfani da na’uran dake taimakawa wajen kara sauti.

7. Mutane miliyan 466 a duniya sun kurmance inda daga ciki miliyan 34 yara kanana ne.

8. Nan ba da dadewa ba farashin samun kula domin hana kurmancewa zai kara tsada a asibitocin duniya.

9. Rashin zuwa asibiti a lokacin da ya kamata.

Share.

game da Author