Wata Sabuwar Karyar Kuma Da Shedanu Suke Yadawa, Wai Kwankwaso ya Kulla alaka da ‘yan Shi’ah, Daga Imam Murtadha Gusau

0

Bismillahir Rahmanir Rahim

Assalamu Alaikum….

Ya ku ‘yan uwa, don Allah ayi mani afuwa, a gafarce ni. Domin ni a gaskiya bani da hakuri da juriyar yin shiru idan naga ana yada karya ko barna!!!

Don Allah ku kalli karyar da ake yadawa, wai su Sanata Rabi’u Musa kwankwaso sun kulla yarjejeniyar hadin baki da ‘yan shi’ah!

Tambayar mu ita ce: Don Allah a ina akayi wannan, ya ku makiya Allah?

To gashi nan dai suna ta yadawa a social media.

Kuma ina son wannan sako ya isa har zuwa ga mai girma Damburam Gombe, tsohon Ministan Abuja, Alhaji Dakta Aliyu Modibbo, domin wannan karyar da ake yadawa, a jaridar Rariya na same ta. Amma kuma wallahi, Allah ya sani, sani na da waye Damburam Gombe, nayi imani da Allah wannan ba ainihin jaridar Rariyar sa bace! Don haka ina mai kira ga Mai girma Damburam Gombe, cewa ya zama wajibi suyi gaugawar daukar matakin kotu, domin yin karar waccan jaridar Rariyar ta bogi, masu yin sojan gona da sunan su!!! Domin a gaskiya suna kokarin bata wa ainihin jaridar Rariya ta gaskiya, mai mutunci da kima a idon al’ummah suna.

Allah ya kyauta, amin.

Ya ku jama’ah ga abunda shedanun nan suke ta yadawa a kafafen yada labarai, da ni kuma na ga cewa ya zama dole in nuna wa al’ummah cewa wallahi karya ne, babu inda akayi wannan, kuma wallahi duk abunda aka fada a wannan shirmen na su soki-burutsun banza ne kawai.

Ga da suke yadawa kamar haka, ku karanta, kuma kuyi hukunci da kan ku:

Taken rubutun nasu na shedanci shine kamar haka:

“DA DUMI DUMINSA; KWANKWASIYYA SUN KULLA YARJEJENIYAR AIKI DA ‘YAN SHI’A.”

Shine suka ci gaba da cewa:

“Labari ya iske mu daga wata majiya mai tushe cewa Jagoran Kwankwasiyya Sanata Rabiu Kwankwaso yana tattaunawa da wasu jiga-jigan Shugabannin Shi’a a Jihar Kano don suyi aiki tare. Idan baku manta ba a zaben Shugaban kasa Jam’iyyar PDP daga sama ta samu gudunmuwa daga kasar Iran tare da goyon baya daga kungiyar Shi’a ta IMN a Nijeriya. Moriyar da ‘Yan shi’a suka sa ran samu shine, da zarar PDP taci mulki zata sako musu Jagoransu Mal. Ibrahim El-Zakzaky. Sanannen abu ne cewa ‘Yan shi’a a jihar Kano suna jin haushin Gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje bisa yadda take goyawa Gwamnatin Tarayya baya a duk sanda rundunar tsaron kasar ta dauki Matakin dakile tare wa ‘Yan kasa hanya da ‘Yan shi’a keyi. Majiyar mu ta tabbatar mana cewa Kwankwaso yayi wa ‘Yan shi’a alkawarin in Gwamnatin Kano ta zama ta Kwankwasiyya to ‘Yan shi’ar zasu samu sakin mara don gudanar da hidimomin su na Addini. Idan ka kalli kungiyar Kwankwasiyya cikin kungiyoyin da ake dasu a siyasa za ka ga dabi’un su sunyi kama dana kungiyar ‘Yan Shi’a. Kungiyar Kwankwasiyya tayi kaurin suna wajen mai da yara da matasa Kangararru tare da kausasa harshe ga Shugabanni da Jagororin Al’umma, wadannan halayen nasu sun samu ne sakamakon irin salo da yanayin yadda Shugaban su Sanata Kwankwaso ke amfani dasu wajen bawa mabiyan nasa horo.
A lokuta da dama Kwankwasawa kan hau titi suyi tattaki ko zanga-zanga a titi kamar yadda matafiya Zariya keyi lokutan bukukuwan su. Babu shakka kungiyar Kwankwasiyya takaddararar kungiya ce da ya kamata Mahukunta da Dattawan Jihar Kano suyi wani yunkuri domin magance matsalolin da wannan kangararriyar kungiya ke haddasawa cikin Jihar mu ta Kano mai Albarka.”

Ya ku jama’ah! Wannan shine karya, sharri, yarfe da kage da suke yadawa domin cimma wata manufa tasu ta sharri, zalunci, murdiya da danniya!

Na ciro wannan rubutu nasu ne, kuma na wallafa a nan, ba tare da na canza, kara ko rage wani abu daga cikin rubutun su ba.

Ya ku jama’ah! Don Allah a ina ne wata jam’iyya ko wani Dan siyasa ya taba yin yarjejeniya da ‘yan Shi’a da wadannan makaryata suke yadawa?

Kuma abun mamaki, wannan karyar fa zaka tarar har da masu kiran kan su malaman addini, zaka samu suna ta yada ta akan mimbarorin wa’azin su da na hudubobin su, kawai saboda dan abunda suke karba wurin ‘yan siyasa! Sun amince suyi wa dan uwan su Musulmi sharri da karya da kage. Don miyar su tayi ja! Amma babu komai, duk dadin abun dai, akwai mutuwa, kuma akwai hisabi.

Ina rokon Allah ya bamu lafiya da zama lafiya a kasar mu Nigeria, da kuma yankin mu na arewa baki daya, amin.

Kuma duk wani da yake kokarin kawo muna tashin hankali, damuwa, zubar da jini, rikici da hayaniya a Nigeria da yankin mu na arewa mai albarka, idan masu shiryuwa ne, Allah ya ganar da su, domin su gane, su daina abunda suke yi, domin mu samu zaman lafiya mai nagarta, mai dorewa, amin.

Dan uwan ku:

Imam Murtadha Muhammad Gusau ne ya rubuta, daga Okene, Jihar Kogi, Nigeria. Za’a iya samun sa a: gusaumurtada@gmail.com ko kuma a 08038289761.

Share.

game da Author