Wata mata mai ciki na neman sanin matsayin aurenta da mijinta a Kotu

0

A ranar Alhamis ne Fatima Salisu mai cikin wata takwas kuma mai shekaru 24 ta shigar da kara a kotun shari’a dake Magajin Gari a jihar Kaduna domin sanin matsayin aurenta da mijinta Jibril Umar.

Fatima ta bayyana cewa mahaifinta ya fada mata cewa Jibril mijinta ya sake ta bayan zama da iyayenta da magabatan Jubril suka yi ranar 18 ga watan Janairu.

” Dama can mun sami sabani tsakani na da Jibril da hakan ya sa iyaye suka shiga maganar.

” Mahaifina ya bayyana mun cewa matsayar da aka cimma a wannan zama da aka yi shine Jibril ya sake ni kuma shi Jibril bai ce komai ba game da wannan matsaya.

Shi kuwa Jibril ya tabbatar wa kotu cewa ya sami sabani da matarsa ne bayan ta nemi ta koma gida ta haihu.

” Ni ban saki matata ba domin ko da suka ce wai na sake ta ban ce komai domin ban fadi ba kuma ban bata takarda ba.

Alkalin Kotun Sa’ad-Gom ya umurci Jibril su bayyana da magabatan su domin kawo karshen wannan matsala.

Share.

game da Author