Wani dan majalisar dokokin jihar Filato da aka riga aka bayyana ya lsahe zaben sa ya rasu da yamman lahadi.
Dan majalisan mai suna Ezekiel Afon, mai wakiltar yankin Pengana a majalisar jihar ya rasu ne bayan fama da yayi da ‘ya gajeruwar rashin Lafiya.
Kakakin jam’iyyar APC na jihar Filato, Bashir Sati ya tabbatar da rasuwar Ezkiel cewa tabbas jam’iyyar za ta yi matukar rashin sa.
” Duk da dai cewa ya dan yi fama da rashin lafiya, rasuwar sa ya girgiza mu.” Inji Bashir.
Discussion about this post