Wani dan kunar bakin wake ya kashe kansa da wani a kofar coci a jihar Adamawa

0

A yau ne wani dan kunan bakin wake ya kashe kansa da wani mutum a kofar cocin kauyen Shuwa dake karamar hukumar Madagali a jihar Adamawa.

Wani da abin ya faru a gaban sa ya bayyana wa manema labarai cewa wannan abin takaici ya faru ne da karfe 7:30 na safiyar yau lahadi.

” Akwai alamun cewa wannan dan kunar bakin waken ya zo ya kashe mutanen dake zuwa wannan coci ne amma kafin ya kai ga shiga cocin bom din ya tashi.

Bom din ya kashe dan kunar bakin waken da wani mutum dake tsaye a kusa da kokar cocin.

Share.

game da Author