A karon farko a zaben 2019 an samu wanda ya amince da kayin da ya sha ya kira wanda yayi nasara domin yi masa murna.
A yau Lahadi ne tsohon gwamnan jihar Sokoto, sanata Aliyu Wamakko da dan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar APC Aliyu Ahmad suka kira gwamnan jihar kuma wanda ya lashe zaben gwamna da aka yi Aminu Tambuwal domin ya masa murna lashe zaben.
Idan ba a manta ba Dan takarar gwamnan jihar Sokoto, kuma gwamna mai ci sannan tsohon kakakin majalisar tarayya, Aminu Tambuwal ya doke dan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar APC Ahmad Aliyu da kuri’u 341 kacal.
Jim kadan bayan canja sheka da yayi, sai jagoran APC a Sokoto, sanata Aliyu Wamakko ya tsaida mataimakin Tambuwal din a wancan lokaci Ahmad Aliyu a matsayin dan takaran gwamna na jam’iyyar APC.
Abin dai da kamar wuya domin tun a karon farko abin ya gagari Tambuwal sai da aka kai ga zagaye ta biyu.
A zagayen zaben da aka gudanar a wuraren da aka soke zabuka, idan Tambuwal yayi nasara a nan sai Aliyu ya yi nasara a can. Abin dai da kamar wuya.
Bisa ga sakamakon da aka bayyana a garin Sokoto Tambuwal ne ya yi nasara a zaben amma fa da kuri’u 341 kacal.
Tambuwal na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 512,002 shi kuma Ahmad Aliyu na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 511,661. Kuri’u 314 ya raba su.