Asusun tallafawa kananan yara na majalisar dinkin duniya (UNICEF) ta bayyana cewa ta horas da mata 25 a karamar hukumar Malumfashi a jihar Katsina yadda ake dinka audugan mata na al’ada.
Jami’in WASH, Job Ominyi ya sanar da haka a taron horas da mata kan yadda ake dinka auduga al’ada na mata da suka yi a Makurdi jihar Benuwai ranar Talata.
Ominyi ya bayyana cewa asusun za ta horas da matan ne domin basu damar iya kula da kan su musamman lokacin da suke jini na al’ada da kuma tsaftace muhallin su.
Ya ce horaswan zai wayar da kan mata game da mahimmancin tsaftace jikin su da muhallinsu, ka’idoji da irin abubuwan dake maido musu da hannun agogo baya game da haila da amfani da darasin dinka audugan al’ada da suka koya a matsayin sana’a.
” Mun kuma dauki lokaci wajen wayar da kan maza kan yadda za su rika tallafa wa matan su a lokacin da suke haila.
Discussion about this post