Tun muna kanana mahaifin mu ke lalata da mu – Inji wasu ‘yan mata biyu

0

Wasu ‘yan mata biyu sun bayyana a kotun dake Ikeja jihar Legas yadda mahaifin su ke lalata da su a duk lokacin da mahaifiyar su bata nan a gida.

Ofishin ‘yan sandan dake Marogbo ne ta shigar da karan yadda mahaifin wadannan ‘yan matan ya yi kokarin kashe mahaifiyar wadannan yara.

Daya daga cikin ‘yan matan mai shekaru 25 ta bayyana a kotu cewa mahaifinsu mai suna Gabriel Ogbar ya fara lalata da ita ne tun tana shekara 12 a gidan su dake Atura a Badagry.

Ta ce mahaifiyar su ‘yar kasuwance da hakan ya sa bata dawowa gida sai dare sannan shi mahaifinsu direban tasi ne inda haka ya sa muke zama a gida tare da shi.

” Duk dare mahaifina kan shigo dakin da muke kwance dauke da wuka ko kuma wani makami inda bayan yayi barazanar kashe ni ne yake danne ni.

” Wata rana da ya shigo yin lalata da ni sai na gudu zuwa cocin mu na kai karan sa ga faston cocin sannan na ki komawa gida har sai da mahaifiyar mu ta dawo gida.

” Mahaifiyata bata dauki mataki komai ba duk da cewa faston cocin mu ya bayyana mata abin dake faruwa tsakani na da mahaifin mu.

‘‘Da tura ta kai bango sai na kwaurace wa gidan mu na tsawon shekara daya.

Yarinya ta biyu ta ce bayan yayansu ta bar gidan ne mahaifin nasu ya fara danne ta da karfin tsiya. A lokacin shekarun ta 10.

” Wata rana da ya zo yin lalata da ni sai na gudu na kai kara a ofishin ‘yan sandan dake Iba sai dai kuma basu yi komai akai ba bayan mahaifin namu ya karyata karar da ana shigar.

” Idan na dawo makaranta na kan wuni gidan abokai na ne sai dare ya yi kuma na tabbata mahaifiyar mu ta dawo sannan na ke komawa gida.

Wata rana da dare bayan mahaifiyar mu ta dawo gida sai muka bayyana mata yadda mahaifin mu ke yi da mu. A nan ne fa muka ta saka baki. Shi ko ya fusata ya yi mata dukan tsiya har ya dauko jarkan fetur zai babbaketa.

Alkalin Kotun ya dage karan zuwa 23 ga watan Mayu.

Share.

game da Author