TSAUTSAYI: Bene mai hawa uku ya rufta da mazaunan cikin sa

0

Wani bene mai hawa uku da aka tabbatar da cewa ana amfani da shi a matsayin wata makaranta, ya rufta wadanda ake cikin sa da yawa.

Al’amarin ya faru ne a kan titin Massey Street, a cikin Karamar Hukumar Lagos Island, da ke Legas.

An ce benen ya rufta ne a yau Laraba da misalin karfe 10 na safe.

Rahotanni sun tabbatar da cewa akwai mutane da dama cikin sa, har da daliban da ke karatu a lokacin da aka hakkake cewa daliban a kan bene hawa na uku su ke.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa an zaro dalibai 10 daga cikin durdushin ginin da ya rufta din.

Ya zuwa lokacin da ake hada wannan rahoto ba a san iyakacin wadanda suka rasa rayukan su ba, domin jami’an Hukumar Agajin Gaggawa ta LASEMA ba su dade da dira wajen ba.

Share.

game da Author