TARON AHAIC2019: Kasashen Afrika na taron tattauna yadda za a inganta fannin kiwon lafiya a Kigali, Rwanda

0

Amref Health Africa da Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Rwanda sun shirya taro domin tattauna yadda za a tunkari kalubalen da kasashen Afrika ke fama dasu dake kawo cikas wajen samar wa mutanen yankin kiwon lafiya.

Ma’aikatan fannin kiwon lafiya, Shugabannin kasashen Afrika, ma’aikatan kafafen yada labarai, Kungiyoyi masu zaman kansu daga kasashen Afrika ne suka halarci wannan taro da aka fara ranar Litini a Kigali kasar Rwanda.

Idan ba a manta ba a shekaran 2014 ne kasashen Afrika suka hadu domin tsara hanyoyin inganta kiwon lafiyar a kashenan su.

Shugabannin kasashen Afrikan da suka halarci wannan taro sun yarda su ware kashi daya daga cikin kasafin kudaden kasashensu na duk shekara domin inganta fannin kiwon lafiya a kasashen su.

Domin kawar da irin wadannan matsaloli da samun ci gaban da ya kamata a fannin kiwon lafiyar kasashen Afrika ne ya sa aka shirya wannan taron.

A taron za a tattauna matsalolin da suka shafi hanyoyin dakile yaduwar cututtuka, samar da tsaftattacen ruwa, tsaftace muhalli, inganta kula ga mata masu ciki da wajen haihuwa, karfafa kimiya da fasaha, wayar da kan mutane game da ‘yancin da suke da shi a fannin kiwon lafiya da samun bayanai game da yadda gwamnati ke kashe kudaden da ta ware wa fannin a kasashen Afrika.

Share.

game da Author