Wasu kwararrun malaman asibiti sun koka kan yadda rashin samun isassun asibitocin kula da masu fama da cutar tarin fuka ke yi wa yaki da cutar kafar angulu a kasar nan.
Malaman asibitin sun koka da haka ne a taron samun madafa game da cutar da aka yi a Abuja, Najeriya.
Tarin fuka cuta ce da ake iya kamuwa da ita idan aka shaki kwayoyin cutar ‘Bacteria’ a iska.
Bayanai sun nuna cewa mutum na iya kamuwa da wannan cuta ce idan ana yawan kusantar mai dauke da wannan cuta.
Malaman asibitin sun bayyana cewa rashin samun maganin cutar kai tsaye da asibitocin yin gwajin cutar na daga cikin matsalolin da suka hana kasar nan kubuta daga kangin da take fama dashi game da yaduwar cutar.
Jami’in cibiyar hana yaduwar tarin fuka da kanjamau dake Amurka Odume Betrand yace babban abin takaici shi ne yadda mutane ke yawan dogaro da allurar rigakafin BCG da aka yi wa yara kanana a matsayin maganin kawar da cutar.
Maganin ‘Bacilli Calmette-Guerin (BCG)’ rigakafi ne da ake yi wa yara kanana domin sama musu rigakafin cutar Amma maganin ba ya kare mutum gaba daya daga kamuwa da cutar.
Betrand ya ce zuwa asibiti ayi gwaji da sannan hanzarta kai mutum asibiti a duk lokacin da mutum ya kamu da tarin da ya wuce wata daya yana fama da shi na daga cikin hanyoyin hana yaduwa da guje wa kamuwa da cutar.
Betrend ya kuma kara da cewa ware kudade domin yaki da kawar da cutar musamman a fannin gudanar da bincike domin gano maganin kawar da cutar zai taimaka matuka.
Idan ba a manta ba shekaru 30 kenan Najeriya ke yaki da kawar da wannan cutar amma har yanzu cutar sai kara yaduwa take yi. A yanzu haka a kwai magunguna da dama da aka gano dake ingancin warkar da tarin fuka amma rashin mai da hankali wajen tabbatar da ingancin magungunan ya hana a sami mafita daga kawar da cutar.
Bayan haka jami’in hana yaduwar cutar tarin fuka na kasa Ayodele Awe a nashi tsokacin ya ce rashin wayar da kan mutane game da cutar na cikin dalilan da yasa har yanzu Najeriya ke fama da yaki da cutar.
Bincike ya nuna cewa mutane 18 na rasa rayukansu a dalilin kamuwa da wannan cuta a Najeriya sannan a duniya gaba daya mutane 4500 ne ke rasa rayukan su.
Alamomin tarin fuka sun hada da:
1. Kamuwa da tari wanda ka iya kai tsawon makoni uku ko kuma fiye da haka ana fama da shi.
2. Ciwon jirji.
3. Rashin iya cin abinci da rama.
4. Yin kaki da jini musamman a lokacin da ake tari.
5. Zazzabi da jin sanyi
6. Yawan jin gajiya a jiki.
7. Yin zufa da dadare.
8. Rashin iya yin numfashi yadda ya kamata.
Discussion about this post