Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta yi kira ga mutane kan yin gwajin cutar tarin fuka domin a dakile yaduwar cutar.
Aisha ta yi wannan kira ne a taron wayar da kan mutane game da cutar da aka yi a kauyen Kpebi dake babbar birnin tarayya Abuja ranar Laraba.
Ta kuma ce gwajin cutar na taimaka wa wajen warkar da cutar da wuri-wuri tun kafin ya yi wa mutum illa.
Bayan haka karamin ministan kiwon lafiya Osagie Ehanire ya koka kan yadda cutar ke ci gaba da yaduwa a kasar nan duk da kokarin kawar da cutar da gwamnati ke yi.
Ya ce rashin samun nasarar kawar da cutar na da nasaba da rashin yin gwaji da karban maganin cutar da mutane ke kin yi duk da cewa hakan duk kyauta ne.
Abubuwa 8 da ya kamata a sani game da tarin fuka.
1. Akan kamu da wannan cuta idan an shaki kwayoyin cuta na ‘Bacteria’ a iska ko kuma idan mai dauke da cutar ya yi tari.
2. Za a iya samun kariya idan ana yin allurar rigakafin cutan.
3. Yin gwajin cutar na cikin hanyoyin gano cutar da wuri da zai taimaka wajen warkewa daga ciwon.
4. Rashin mai da hankali wajen shan magungunan cutar na hana ciwon warkewa.
5. Kamuwa da cutar kanjamau na cikin hanyoyin kamuwa da cutar.
6. Kamata ya yi idan mutum ya kamu da tari da ya kai makoni biyu yana fama da shi ya nemi likita .
7. Mai dauke da wannan cutar zai yi fama da rashin iya cin abinci,ciwon kirji zazzabi da sauran su.
8. Za a iya samun karin bayani game da cutar daga wajen kwararrun malaman asibiti a wannan lanbar 08002255282.