Masu Sa-ido kan zabe da Tarayyar Turai ta tura domin ganin yadda aka gudanar da zaben da aka maimaita a Kono, ta ce tarzoma, hargitsi da cinikin kuri’u ne suka yi tasiri a zaben na Kano.
Tarayyar Turai ta bayyana haka bayan nazarin wakilan ta su 20 da ta tura Kano domin zame mata idon kallon yadda aka gudanar da zaben, a ranar Asabar 23 Ga Maris, a Jihar Kano.
Kungiyar ta kuma nuna rashin jin dadin yadda aka hana wakilan ta da ta tura Kano samun damar shiga wasu wurare domin gane wa idanun su irin wainar da aka rika toyawa a lokutan da ake gudanar da zaben.
“An samu gagarimar matsalar tsaro, yayin da wasu gungun masu dauke da muggan makamai suka kai wa jama’a hari, tare da firgita su.
“Sannan kuma jami’an tsaro bas u gudanar da aikin su kamar yadda ya dace su yi ba, a matsayin su na masu kare lafiya da rayuwar wadanda suka fita domin yin zabe.”
Haka dai Tarayyar Turai ta bayyana a cikin wani sako rubutacce da ta aiko wa PREMIUM TIMES jiya Litinin da rana.
Kunyiyar ta ce ba wakilan ta masu sa-ido kadai aka hana shiga wasu wuraren ba, har ma da wasu ‘yan jaridu.
Ta kuma nuna damuwar ta ganin har aka yi zaben a Kano aka gama, a ranar zaben INEC ba ta yi wani jawabi ko tsokaci a kan tashe-tashen hankula, farmaki da cinikin kuri’u da aka rika yi a Kano ba.
Ta kara nuna damuwar ta a kan yadda matasa dauke da muggan makamai da suka hada da adduna da takubba, gorori da barandami suka rika cin karen su babu babbaka a kan titinan Kano a ranar zabe, ba tare da jami’an ‘yan sanda ko INEC sun yi wani hobbasa na dakile su ba.