Dan takarar gwamnan jihar Sokoto, kuma gwamna mai ci sannan tsohon kakakin majalisar tarayya, Aminu Tambuwal ya doke dan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar APC Ahmad Aliyu da kuri’u 341 kacal.
Jim kadan bayan canja sheka da yayi, sai jagoran APC a Sokoto, sanata Aliyu Wamakko ya tsaida mataimakin Tambuwal din a wancan lokaci Ahmad Aliyu a matsayin dan takaran gwamna na jam’iyyar APC.
Abin dai da kamar wuya domin tun a karon farko abin ya gagari Tambuwal sai da aka kai ga zagaye ta biyu.
A zagayen zaben da aka gudanar a wuraren da aka soke zabuka, idan Tambuwal yayi nasara a nan sai Aliyu ya yi nasara a can. Abin dai da kamar wuya.
Bisa ga sakamakon da aka bayyana a garin Sokoto Tambuwal ne ya yi nasara a zaben amma fa da kuri’u 341 kacal.
Tambuwal na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 512,002 shi kuma Ahmad Aliyu na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 511,661. Kuri’u 314 ya raba su.
Yanzu dai ana jiran malamin zabe ya bayyana Tambuwal a matsayin wanda ya lashe zaben.