TAMBAYA: Idan mutum ya yi wankan janaba sannan yayi na sabulu zai iya yin sallah Kai tsaye? Tare da Imam Bello Mai-Iyali
AMSA: Alhamdu-lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.
Musulmin da yayi wakan Janaba sannan yayi wakan sabulu, wankansa ya yi, kuma babu laifi yayi Sallah kai tsayi, idan yayi alwala kuma bai
shafi azzakarinsa ba lokacin wankan sabulun. Shafan zakari da cikin tafin hannu yana warware alwala. Domin haka, sai maza su kiyaye. Idan
sun shafi al-aura, to sai sun sake alwala.
Babu laifi mutum yayi wankan tsarki bayan yayi wakan sabulu, kamar yadda zai iya yin wankan tsarki sannan yayi wakan sabulu. Wakan tsarki
ana yinsa ne da ruwa mai tsarki kuma mai tsarkakewa, wato ruwan da dandanonsa bai canza ba, launinsa bai canza ba kuma kamshinsa bai
canza ba.
Idan mai wanka zai fara wankan ibada kafin na sabulu, to babu wani khaufi dangane da ruwansa, saidai yakiyaye kar yashafi azzakarinsa
bayan alwala. Amma idan mai wanka zai fara na sabulu ne, to ya kiyaye ruwansa kar ya gurbata da kumfar sabulu har ya canza launinsa, ko
kamshinsa, ko dandanonsa.
Allah ya tsare-mana ibadar mu kuma ya karba mana. Amin.
Discussion about this post