Hukumar Shirya Jarabawar Kammala Sakandare ta Afrika ta Yamma (WAEC) ta bayar da sanarwar sakamakon jarabawar da dalibai suka rubuta ta WASSCE, cikin watan Janairu da ya gabata.
Wannan ne karo na biyu da aka kara samun gagarimar rashin nasara tun daga lokacin da aka fito da tsarin jarabawar a cikin 2018.
Yayin da ake bayyana sakamakon jarabar a Ofishin Hukumar na Kasa da ke Lagos, shugaban hukumar na Najeriya, Isaac Adenipekun ya ce dalibai 12,202 ne suka yi rajista, amma 11,892 ne suka rubuta jarabawar.
Adenipekun ya ce mutum 3,102 ne kadai ya samu sakamakon darussa biyar abin da ya yi sama da suka hada da Turanci da lissafi.
Ya ce a gaskiya an fadi jarabawar sosai.
Ya kuma tunatar da cewa a shekarar da ta gabata, wato Janairu, 2018, kashi 17.5 ne kacal suka samu nasarar darussa biyar ko sama da haka da suka hada da Turanci da kuma lissafi.
Ya ce ko a 2018 din dlibai 11,000 ne suka rubuta jarabawar.
A wannan ta 2019 kuwa, ya ce dalibai maza 6,180 ne suka rubuta jarabarwar, yayin da mata kuma su 5,712 ne.
Adenipekun ya ce an rike sakamakon jarabawar dalibai sama da 300, saboda akwai zargin magudi ko satar jarabawa da ake yi musu.