SOKOTO: Jam’iyyu 28 sun ki amincewa da nasarar Gwamna Tambuwal

0

Gamayyar wasu jam’iyyu 28 a Jihar Sokoto sun bada sanarwar kin amincewa da nasarar da dan takarar PDP a zaben gwamna, Aminu Tambuwal ya samu.

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta bayyana cewa Gwamna Tambuwal ne ya yi nasara a kan dan takarar APC da bambancin kuri’u 342 kadai.

Da suke jawabi a gaban manema labarai, shugaban gamayyar jam’iyyun mai suna Musa Aiyu na jam’iyyar NEPP, ya bayyana kin amincewar su da sakamakon zaben.

Musa Aliyu wanda shi ne dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar NEPP a Jihar Sokoto, ya bayyana cewa an yi tashe-tashen hankula kuma an yi asarkala da kumbiya-kumbiya a lokacin zaben.

Wadannan kuwa a ta bakin sa, ya ce duk sun kauce wa dokokin zabe da kuma dokar kasa.

“Sannan kuma mun lura da cewa a zabukan da aka maimaita an cinikin kuri’u rututu, an razana jama’a, wasu wurare ba a yi amfani da na’urar ‘card reader’ ba, wasu sun jefa kuri’a sau biyu. Wato a wasu rufunan zaben sau biyu aka yi zabe.

Daga nan sai suka ce su na goyon bayan jam’iyyar APC da ta nemi hakkin ta a kotu.

Wasu daga cikin wadanda suka halarci taron har da Mujjitaba Aminu na jam’iyyar MPN, Muhammad Sheku na GPN, Lawali Haliru na UPP, Dan-Ali Kasarawa na LP da kuma Bello Ibrahim na DPP.

Sai dai kuma ita jam’iyyar APC da ta zo ta biyu, tuni tun a ranar da aka bayyana sakamakon zabe dan takarar gwamna a karkashin ta da kuma jigon jam;iyyar a Sokoto, Sanata Aliyu Wamakko suka taya Tambuwal murna.

Share.

game da Author