Rahottani sun tabbatar da cewa Boko Haram sun kai wani hari tare da kokarin shiga garin Michika da karfinn tsiya.
Sai dai kuma sun hadu da jajircewar sojojin Najeriya, wadanda suka tare su aka yi gumurzu sosai.
Hakan ya faru ne jiya Litinin da dare.
Kuma an ce an kwashe sa’o’i masu yawa ana barin wuta a tsakanin bangarorin biyu.
Sojoji sun samu galabar fatattakar Boko Haram a kokarin da suka yi na kutsawa garin Michika.
Michika gari ne mai albarkacin kasuwanci a jihar Adamawa.
Wasu mazauna garin Michika sun shaida cewa sun fara jin karar manyan bindigogi ne tun wajen 7 na dare a kan hanyar Michika zuwa Lassa, a yayin da Boko Haram suka nausa suka nufi garin na Michika.
Sai dai kuma sun yi taho-mu-gama da sojojin Najeriya a daidai lokacin da suka kusa shiga garin. Haka wani mai suna Idris ya shaida.
Shi ma wani mai suna John Jigalambu, wani mazaunin kauyen Bazza da ke kusa da Michika, ya ce sun rika jin karar harbin bindiga.
Ya ce tilas mutanen kauyen su suka arce kowa ya tsere domin gudunn kada a kashe shi.
Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Adamawa, Ahmad Sajoh ya tabbatar da harin, kuma ya ce amma sojoji sun ci galabar su.
Ya ce Boko Haram sun yi kokarin shiga Michika ne bayan sun biyo ta kauyen Kirchinga da ke kusa da Karamar Hukumar Madagali.
Ya ke kafin sojoji su kore su, sai da suka kone First Bank na Michika sannann kuma suka banka wa wasu shaguna wuta.