Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa ta kama mutane 24 da suke da alaka da sace akwatunan zabe da garkuwa da mutane a jihohin Abia, Imo da Ribas.
Kakakin rundunar Sagir Musa ya sanar da haka a wata takarda da ya raba wa manema labarai ranar Talata inda ya kara da cewa sun kama mutane 15 daga cikin mutanen 24 a jihar Abia.
Ya ce daga cikin mutane 15 din da suka kama biyar ‘yan jagaliya ne da ‘yan siyasa ke amfani da su domin tada rikici a lokacin zabe.
Musa ya ce dakarun sojojin sun kama wasu mutane shida a hanyar Osisioma dauke da takardun zaben da aka riga aka dangwala su.
Bayan nan kuma sojojin sun kama wasu masu garkuwa da mutane da suka sace wani ma’aikacin INEC.
” A nan dai sojojin sun samu nasarar kama masu garkuwa hudu daga cikin su sannan sauran suka gudu. Sannan mun mika wadannan mutane hudu ga ‘yan sanda sannan muna nan muna farautar sauran da suka gudu.
A jihar Imo sojoji sun kama wasu sojojin boge dake raka wata ‘yar siyasa a hanyar Everyday Super Market a Owerri.
A karshe Musa yace sojoji sun ceto wani mutum mai suna Authur Nkama a karamar hukumar Odukpani da aka yi garkuwa da shi a Ikot jihar Ribas.