Shugabannin jam’iyyar APC na yankin Kudu maso Kudu sun fara neman kamun-kafar mukamin shugabancin majalisar dattawa a hannun Shugaba Muhammadu Buhari.
Sun mika wannan kokon-bara ne a lokacin a cikin sakon taya murnar da suka yi wa Buhari na sake lashe zabe karo na biyu da aka gudanar ranar 23 Ga Fabrairu.
Sakon ya na kunshe ne cikin wani rahoto da jaridar PUNCH ta buga.
Duk da cewa Buhari ba shi da ikon nada wa majalisa shugaba, zai iya yin amfani da mukamin sa ya nemi alfarma. Sai dai kuma mukaman siyasa manya irin wadannan aka raba su ne ga shiyyar da ake gani ta na da tasiri ko ta yi tasiri a lokacin zabe.
APC ce za ta fitar da Shugaban Majalisar Dattawa, domin ta fi PDP yawa a majalisar.
A cikin wata sanarwa da Mataimakin Shugaban APC shiyyar Kudu-maso-kudu, Ntufam Etta ya ce shiyyar su ta cancanci a ba ta mukamin shugaban majalisar dattawa.
Ya ce shugabannin jam’iyyar sun yi kokarin dawo da martabar shiyyar ta hanyar samar da kasuwanci da kuma wayar da kan matasan yankin cewa sai da wanzuwar zaman lafiya yankin zai iya samun ci gaba.
Ya ce a yankin yanzu an daina tawaye kuma an daina tashin-tashina. Matasa sun rumgumi turbar wanzar da zaman lafiya.
Ya ce ya tuna lokacin da dan shiyyar ta su Joseph Wayas ya yi shugabancin Majalisar Dattawa, ya shahara kuma ya inganta turbar dimokradiyya a siyasar kasan nan.