SHUGABAN MAJALISA: APC ta maida wa Ndume martani, tace tana nan kan bakanta na zabin Ahmed Lawan

0

Jam’iyyar APC ta maida wa sanata Ali Ndume martani cewa ba za ta canja zabin Ahmed Lawan da ta yi ba na zama shugaban majalisar dattawa.

Lanre Issa-Onilu ne ya bayyana matsayin jam’iyyar da ya ke zantawa da manema labarai a hedikwatar jam’iyyar ranar Laraba.

” Jam’iyyar APC ta riga ta tsayar da zabin ta. Babu wani rudani da wani zai kawo mana a jam’iyyar. Ahmed Lawan ne kowa zai bi. Sannan kuma muna da yawan da yanzu ba zamu yi shugabanci tare da jam’iyyar PDP ba. kowa a tsaya a matsayin sa.

” APC na da sanatoci har 60 yanzu da hakan ya sa ko zabe ba za ayi ba ma ranar rantsar da majalisar. Ko kuri’ar PDP daya bamu bukata. suje can su zabi wanda suke so. Mu kawai mun isa.

Lanre ya kara da cewa hakan ma shine jam’iyyar ta tsayar a majalisar wakilai ta tarayya.

Idan ba a mata ba Sanata Ali Ndume ya bayyana ra’ayin sa na neman kujeran shugaban majalisar dattawan. Sai dai kuma wannan bukata ta sa da kamar wuya domin bayan haka jam’iyyar da shugaban kasa Muhammadu Buhari da kan sa sun fidda Ahmed Lawan a matsayin zabin su.

Sai dai kuma Ndume ya ce bai gamsu da wannan shawara da da jam’iyyar APC ta dauka ba cewa har yanzu yana nan kan bakar sa.

Share.

game da Author