Kungiyar kiwon lafiya ta duniya za ta fara amfani da na’ura dake iya gano cutar shan-inna a yara.
Na’urar na kuma iya gano cututtuka kamar su bakon dauro,kwalara,kanjamau da shawara.
Wasu jami’an kungiyar Korea International Cooperation Agency (KOICA) da suka kirkiro wannan na’uran sun nuna wa WHO yadda ake amfani da na’urar a ofishin ta dake Brazzaville Jamhuriyyar Kongo.
WHO ta bayyana cewa amfani da wannan na’ura zai taimaka wajen ganin an kawo karshen cutar a kasashen Afrika.
Idan ba a manta ba bincike ya nuna cewa kasashen Najeriya, Afghanistan da Pakistan ne kasashen da suka rage a duniya da har yanzu suke fama da cutar shan inna.
Bincike ya nuna cewa rashin yin allurar rigakafin wannan cutar ga yara a yanikin Arewa maso Yammacin Najeriya na cikin matsalolin da ya sa ba a iya kawo karshen cutar a kasar nan ba da haka na da nasaba ne da aiyukkan Boko Haram da ake fama da shi a yankin.
” Duk da cewa Najeriya ta sami nasarori da dama wajen dakile yaduwar cutar shan inna amma amfani da wannan na’ura zai taimaka wajen kawar da cutar a yankunan da ake fama da hare-haren Boko Haram.