SAKAMAKON ZABE: An kafa dokar hana fita awa 24 a Jalingo

0

Gwamna Darius Ishaku na Jihar Taraba ya kakaba dokar hana fita ta awa 24 a Jalingo, babban birnin jihar Taraba.

Wannan jawabi na kunshe ne cikin wata sanarwa da Babban Kakakin Yada Labaran Gwama, mai suna Bala Dan Abu ya fitar a ranar Litinin.

Gwamna ya umarci dukkan jami’an tsaro su tabbatar da tilasta jama’a yin amfani da wannan doka.

Sanarwar ta ce an kakaba dokar ne har sai yadda hali ya yi.

NAN ya ruwaito cewa garin Jalingo ya barke da murnar sanar da nasarar lashe zabe da Ishaku ya yi a karkashin jam’iyyar PDP a karo na biyu.

Sai dai kuma murnar cin zabe ta hautsine yayin da matasa suka fara jifa da duwatsu kuma suka rika lalata kayayyaki.

Share.

game da Author