RIKICIN KADUNA: El-Rufai ya kafa dokar hana walwala a Kajuru

0

Gwamnatin Jihar Kaduna ta kafa dokar hana walwala a Karamar Hukumar Kajuru da ke cikin jihar.

Haka wata sanarwa da aka fitar ta nuna, wadda kakakin yada labarai na gwamna, Samuel Aruwan ya sa wa hannu a madadin gwamna.

PREMIUM TIMES ta bada rahoton yadda aka rika karkashe mutane a Kajuru a cikin wata daya da ya gabata.

An rika yin kashe-kashen ne cikin kauyuka da rugage. Kashe-kashe na baya-bayan nan ya afku cikin satin da ya gabata.

Aruwan ya kara da cewa an kuma kakaba dokar hana fita ne a wasu garuruwa ko kauyuka da shafi cikin karamar hukumar Chikun.

“ Sanarwar ta ce bayanai na tsaro da aka samu daga yankin ne suka tilasta kafa dokar ta-baci a yankin daga shida na yamma har zuwa wayewar gari, babu walwala.

“ Dokar ta fara ne daga yau Laraba, 13 Ga Maris, 2019, kuma ta shafi Kujama da Maraban Rido da ke cikin Karamar Hukumar Chikun.

Ya ce an sa dokar daga karfe 6 na yamma zuwa karfe 6 na safe a kowace rana.

Ya ce an umarci jami’an tsaro su tabbatar da ana bin dokar, kuma an yi kira ga jama’a su bi doka.

Share.

game da Author