Rikici ya sake tirnike jam’iyyar APC, kwanaki biyu bayan nasarar da Shugaba Muhammadu Buhari ya samu ta sake zaben sa karo na biyu da aka yi.
Ana ganin cewa Buhari ne kadai tsintsiyar da ta daure bangarorin APC, wadanda tun kafin zabe jam’iyyar ta dare daban-daban.
Dama kuma tun kafin zaben shugaban kasa, gwamnoni biyu, Rochas Okorocha na Imo da kuma Ibikunle Amosun na Ogun, duk sun ce ba za su mara wa ‘yan takarar gwamnan da APC ta tsaida domin su gaje su ba.
Okorocha da Amosun dai sun tsaya takarar sanata a karkashin APC kuma duk sun yi nasara.
Su biyun wa’adin mulkin su na gwamna zai kare a ranar 29 Ga Mayu, 2019.
Sauran wadanda aka dakatar baya ga Okorocha da Amosu, su ne Ministan Harkokin Neja Delta, Usani Usani da kuma Darakta-Janar na Muryar Najeriya, Osita Okechukwu.
Uwar Jam’iyyar ta kasa ce ta amince da dakatarwar da aka yi musu bayan sun nuna rashin goyon bayan ‘yan takarar gwamnan jihar su.
Da ya ke maida martani, Okorocha ya ce Shugaban Jam’iyyar APC, Adams Oshimhole ya wuce makadi da rawa a shirmen siyasar da ya ke yi.
Ya ce Oshiomhole na kokari ne kawai ya kashe jam’iyyar APC a yankin Kudu maso Gabas.
Okorocha ya ce Oshiomhole ya na dagula gangar siyasar 2023 ce tun yanzu, alhali kuma ya na sane da cewa an yi murdiya da babakere a zaben 2019.
Yayin da Okorocha da Okechukwu ke ta kokarin a maida mulki a hannun kabilar Kudu maso Gabas, a 2023, su ma bangaren Kudu maso yamma sun a ta korari ta hanyar Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo da kuma Bola Tinubu.
Idan har Okorocha ya kara dadewa a cikin APC, to zai iya neman shugaban kasa daga bangaren Kudu maso Gabas.
Cikin sanarwar da Okorocha ya fitar, ya bayyana irin muhimmiyar rawar da ya taka wajen kafa jam’iyyar APC.
Ya yi wa Oshiomhole kaca-kaca dangane da goyon bayan da ya bayar wajen tsaida Hope Uzodinma dan takarar APC na jihar Imo, duk kuwa da cewa akwai tukume-tuhume biyar da EFCC ke yi masa, bayan kwace masa takardar iznin fita, wato biza.
“In banda shirmen Adams Oshiomhole, ta ya zai dakatar da gwamnonin APC daga jam’iyya, kwana biyu kacal bayan samun nasarar da APC din ta yi, kuma wadannan gwamnonin duk sun yi kokari a jihohin su a zabukan shugaban kasa da majalisa sannan duk sun yi nasara?
“Sannan kuma Oshiomhole na jin tsoron kada Gwamna Okorocha ya samu wani babban mukami a Majalisar Tarayya idan ya shiga a matsayin sa na sabon sanata.”
“To Oshiomhole ya sani cewa sai APC a yankin Kudu maso Gabas ta fi Oshiomhole karko a cikin jam’iyyar. Za a dade ana gogawa da APC a wannan yankin, amma Oshiomhole karkon-kifi zai yi a cikin APC.
Sai dai kuma shi Osita Okechukwu ya shaida cewa har yanzu ba a aika masa da takardar shaidar dakatarwar da jamiyyar APC ta yi masa ba.
Ya ce da shi aka yin kamfen ba ji ba gani domin tabbatar da cewa Buhari ya sake lashe zaben da ya gudana a cikin makon da ya wuce.
Ya ce kuma shi ne ya rika kashe kudade wajen yin tallace-tallace a shafukan jaridun yankin Kudu maso Gabas. Don haka don APC ba ta tabuka abin a zo a gani a yankin ba, ba su za a ga laifi ba.