RIBAS: Dan takarar mataimakin gwamnan AAC, jam’iyyar da Amaechi ya daure wa gindi, ya koma bayan Gwamna Wike

0

Dan takarar mataimakin gwamnan AAC, jam’iyyar da Amaechi ya daure wa gindi, ya fice sauka daga takara tare da ficewa daga jam, iyyar ya koma PDP, bayan Gwamna Wike.

Akpo Yeeh, shi ne dan takarar mataimakin gwamna a karkashin AAC, wadda Ministan Harkokin Sufuri, Rotimi Amaechi ya daure wa gindi, bayan da Kotun Koli ta haramta wa jam’iyyar APC shiga dukkan takarar mukamai a jihar Ribas.

Har ya zuwa yau dai ba a kai ga kammala zaben gwamna da na majalisar dokokin jihar Ribas ba.

Yayin da Gwamna Nyesom Wike ke neman sake mikewa a kan kujerar sa karkashin jam’iyyar PDP, shi kuma Amaechi sai kai-gwauro-da-mari ya ke yi domin ganin ko ta wane hali Wike bai sake hawa kujerar gwamnan ba.

Wannan ya haifar da tashe-tashen hankula har da kashe-kashe da kekkata kuri’u da takardun tattara sakamakon zabe.

An kuma yi zargin cewa Amaechin ya yi amfani da jami’an sojoji wajen kokarin hargitsa zaben.

Sojoji dai sun musanta wannan zargi da aka yi musu.

A jiya Litinin ne Yeeh ya kai ziyara Gidan Gwamnatin Jihar Ribas, a Fatakwal, inda ya tabbatar wa Wike cewa ya fice daga AAC, koma PDP, jam’iyyar da Wike ya ke ciki.

“Ba zan ci gaba da kasancewa ina bin titi maras saurin kai gaci ba, alhali ga titin da ya kamata na bi domin na isa inda zan je da wuri.”

Haka ya fada wa Gwamna Wike a gaban Uche Secondus, Shugaban Jam’iyyar PDP na Kasa.

Jaridar Sahara Reporters, wadda mawallafin ta, Omoleye Sowore ne dan takarar shugaban kasa a zaben da aka gudanar cikin Maris, 2019, ta ruwaito Mista Yeeh ya na cewa Amaechi ya kwace musu jam’iyya sai sai harbat-ta-Mati ya ke yi a ciki.

INEC dai ta bada sanarwar ci gaba da tattara sakamakon zabe a ranakun 2 zuwa 5 Ga Afrilu.

Share.

game da Author