Kungiyar Kwallon Kafa ta Real Madrid da ke Spain ta mika kokon barar neman sayen fitaccen dan wasan Kungiyar PSG ta Faransa, Kylian Mbappe a kan zunzurutun kudi har fan milyan 240 na Birtaniya.
Naira biliyan 114.7 ne daidai da fan milyan 240.
Mbappe, wanda bai wuce shekaru 20 a duniya ba, zai iya kai tsawon shekaru goma ya na jan zaren sa a Madrid. Sai fa idan ya hadu da matsalar yawan jin raunuka a lokutan buga wasanni.
Jaridar France Football da Daily Mail ta Ingila da sauran jaridun Turai masu yawa, sun ruwaito cewa mai horas da Madrid, Zinedine Zidane ya sa wa Mbappe kahon zuka, ta yadda a kullum tunanin sa shi ne yadda zai sayo shi daga PSG ya maida shi Madrid.
Wasu na ganin ba yadda za a yi PSG su amince su sayar da Mbappe, sai dai kuma duk da haka, Real na ji a jikin ta cewa babu abin da kudi ba zai yi magani ba.
Mujallar France Football ta buga labarin kokarin cinikin Mbappe da Zidane keyi, inda ta buga hoton Zidane din da Mbappe a gaban bangon mujallar.
Tun bayan komawar Zidane Madrid a cikin wannan watan ne shugaban kungiyar, Florentino Perez ya ware masa fan milyan 430, domin sayen ko ma wane dan wasa ne ya ke da ra;ayin sayowa a fadin duniyar nan.
An tabbatar da cewa akwai tsabar kudin sayen ‘yan wasa har fan milyan 340 zube a kasa a aljihun Madid. Cikon fan milyan 90 kuma za su fito ne daga cefanar da Gareth Bale da Madrid za ta yi a karshen wannan kakar wasa ga wani babban kulob da ke buga Premier a Ingila.
Real Madrid na neman yin sauye-sauyen ‘yan wasa ido-rufe idan an fara cefanen ‘yan wasa nan ba da dadewa ba.
Kuskuren da ta yin a kin gaggauta wanda zai maye gurbin da Christiano Ronaldo ya bari, ya janyo wa Real asarar La Liga da Champions League a wannan kakar wasa.
Mbappe ya koma PSG daga Monaco cikin kakar 2017. Yanzu shi ke kan gaba a kasar Faransa da yawan kwallaye 34 a wasanni 35 da ya buga a wannan kakar.
Jaridar Marca ta birnin Madrid ta ruwaito cewa kwanan nan Liverpool ta shaida wa Real Madrid cewa ko fan-cika-teku za ta biya, ba za a saida mata Sadio Mane ba.
Har ila yau, Zidane ya kuma maida hankalin sa a kan Edan Hazard na Chelsea.
Sannan kuma Marca ta kara da cewa Zidane na tunanin hadawa da Paul Pogba na Manchester United, matsawar dai idan ya matsa lamba za a sayar masa.