Real Madrid, kungiyar da ke rike da Kofin Zakarun Turai, wato Champions’ League shekaru uku a jere, ta kwashi buhunan kunya a jiya Talata da dare, inda kungiyar Ajax ta bi ta har gida ta yi mata korar-kare daga gasar, da ci 1:4.
Tun bayan tafiyar mai horas da kungiyar, Zinedine Zidane ne Madrid ya afka rami gaba dubu, wanda har yau an kasa samun wanda zai iya ceto ta.
Ficewar shahararren dan wasan ta Ronaldo, bayan tafyar Zidane, ya kara jefa Madrid cikin tsomomuwa. Ronaldo ya koma Juventus da ke kasar Italy.
Cin-kacar da Ajax ta yi wa Madrid har gida Talata da dare, ya kara tabbatar da cewa a yanzu ba ta batun ceto Madrid ake yi daga rami ba, domin Ajax ta bi kungiyar da ruwan duwatsu ta cike ramin da ta fada a ciki, sannan kuma ta sa makulli ta kulle rijiyar.
Hakan na nuni da cewa Madrid ba ta za iya cin ko da kofinn shan shayin gadagi a wannan kakar wasa ba.
A wasan da aka buga na farko cikin makonni biyu a gidan Ajax a Armstaderm, Madrid din ce ta yi nasara da ci 2:1.
A filin Madrid na Barnabeau kuwa, minti shida da fara wasa aka jefa wa Madrid kwallo. Sannan kuma minti 10 bayan wannan aka kara watsa wata kwallon a cikin ragar Madrid.
Bayan dawowa hutun rabin lokaci aka ci Madrid wasu kwallaye biyu.
Cin da aka yi wa Madrid a jiya Talata a gida, shi ne a uku a jere da aka yi wa kungiyar a cikin kwana bakwai.
Barcelona ta ci Madrid 3:0, sannan kuma bayan kwana uku ta kima ta yi mata daya mai ban haushi.
Da aka kara kwana uku kuma, Ajax ta har gida ta yi mata dukan tsiya.
Tun kafin a tashi daga wasan ‘yan kallo suka rika ficewa daga filin saboda kunci, takaici da bakin ciki.
Discussion about this post